1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin komawa ga makamashin Gas

May 15, 2024

A kokarin sauyi daga dogaro da man fetur, Najeriya ta kaddamar da wasu cibiyoyin iskar gas guda Uku da ke da zummar kara yawan iskar gas a cikin gida da kaso 25 cikin dari.

https://p.dw.com/p/4ftm4
Ölgewinnung in Afrika - Symbolbild
Hoto: picture-alliance/A. Holt

Tuni dama Najeriyar ta ayyana shekarun 2020 a matsayin shekarun komawa gas a bangaren kasar da ta kwashe shekaru da dama cikin fatan man fetur amma kuma ke cizon yatsa yanzu.

Cibiyoyin guda uku na Anoh da ke a kauyen Assa a jihar Imo da kuma cibiyar AHL da ke jihar Delta da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar na zaman sabon fata a tsakanin mahukunta kasar da ke takama da artzikin iskar gas din amma kuma ke kona shi tare da gurbata muhalli. Cibiyoyin dai na shirin samar da karin kaso 25 cikin dari na bukatar iskar ta gas domin samar da wuta da takin zamani ko bayan amfanin masana'antu.

Tashar makamashin Gas na Najeriya
Tashar makamashin Gas na NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Tuni dai dama kasar take fadin ta yi nisa a kokarin rikidewa daga hajjar man fetur zuwa iskar gas Mele Kolo Kyari shugaban kamfanin mai na kasar NNPC, ya ce ana shirin ganin amfani a cikin sabon tsarin karkata zuwa iskar gas.

Kokarın komawa Gas din dai ya kai Abujar yanke hukuncin sabbin matakan rage dogaro da hajjar man fetur da ke zaman makamashi mai tsada ga kasar. Kuma kasar a fadar shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kaddamar da sabbabin cibiyoyin guda uku ta dau hanyar ganin daban cikin fatan samun arzikin al'umma.

Bututun makamashin gas na Najeriya
Bututun makamashin gas na NajeriyaHoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Yace wannan batu yana da muhimmanci ga kasarmu, kuma yana tabbatar da kokarin gwamnatinmu na inganta masana'antar iskar gas dinmu domin habbakar makamashi, da samar da cigaban masana'antu da aiyyuka tsakanin al'umma.

Abun farin ciki ne cewar wadannan cibiyoyi na iya samar da kafar iskar gas miliyan 500 a kusan kullum, da kusan dukkanninsa zai kare a kasuwannin gida, adadin da ke nufin karin kaso 25 cikin dari na yawan iskar da muke samarwa yanzu.

Sama da dalar Amurka miliyan 500 ne dai kasar take saran samu daga aiyyukan cibiyoyin gas din guda uku.