1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yakin Isra'ila da Hamas na janyo kalubale

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 8, 2024

Jami'ar The Free ta Brussels a kasar Beljiyam ta yanke shawarar kawo karshen duk wani aikin hadin gwiwa na bincike da take da Isra'ila da suka hadar da na fannin ilimin kirkirarriyar basira.

https://p.dw.com/p/4fe8j
Turai | Beljiyam | Adawa | Isra'ila | Yaki | Zirin Gaza
Yayin da Isra'ila ke ci gaba da barin wuta a Zirin Gaza, ana zanga-zangar adawa a TuraiHoto: Frédéric Metezeau/France Inter/dpa/picture alliance

Kamfanin dillancin labaran Beljiyam din Belga ya ruwaito cewa jami'ar The Free ta Brussels ta cimma wannan matsaya ce, sakamakon yadda yaki ya kara rincabewa tsakanin Isra'ilan da kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin na Zirin Gaza na Falasdinu da ya janyo asarar rayuka masu yawa.