1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A dawo da dukiyar da 'yan siyasa suka sace

Abdullahi Tanko Bala
September 28, 2023

Hadin gwiwar kungiyoyin farar hula na Burtaniya da Najeriya sun bukaci gwamnatin Burtaniya ta mayar wa Najeriya dukiyar da ta kwace daga dan siyasar Najeriya James Ibori wanda ta samu da laifin zamba.

https://p.dw.com/p/4Wvw1
Firaministan Burtaniya Rishi Sunak
Firaministan Burtaniya Rishi SunakHoto: UK Parliament/Jessica Taylor/REUTERS

Kungiyoyin sun bukaci mayar da kudaden ta hanyoyi masu nagarta yadda talakawan Najeriya za su amfana.

A cikin wata wasika da suka aike wa ministocin cikin gida da kuma kasashen waje hadin gwiwar kungiyoyin farar hular da suka kai kimanin hamsin sun ce dogon jinkiri da ake samu na kwace kadarorinna yin karan tsaye ga darasin da ya kamata hukuncin daurin da aka yanke wa Ibori fiye da shekaru goma da suka wuce na cin hanci da rashawa domin zama izina ga na gaba.

Karin Bayani:Hukunci bisa laifin yiwa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa 

Ibori wanda har yanzu yake da tasiri a Najeriya ya sha ganawa da shugaban Najeriya Bola Tinubu a baya bayan nan yana kuma da aminai da ke rike da manyan mukamai.