1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta kai hari a Mogadishu

Abdourahamane Hassane
March 23, 2022

Kungiyar Al-Shabaab ta kai hari a filin saukar jiragen sama na Mogadishu babban birnin Somaliya,inda ke da ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya da na jakadanci da kuma sansanin dakarun Tarayyar Afirka Amisom.

https://p.dw.com/p/48w6v
Somalia | Flughafen Mogadischu
Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Shaidun gani da ido sun ce an yi musanyar wuta a cikin filin saukar jiragen saman a artabun da aka kwashe sao'i ana yi a sa'ilin da wasu mutanen guda biyu dauke da makamai suka kai harin. Akalla an kashe sojin gwamnatin daya yayin da wasu da dama suka jikkata, sai dai kawo yanzu ba a da masaniya kan ko dakarun gwamnatin sun yi nasarar murkushe 'yan ta’addar. A shekara ta 2011 sojojin rundunar kiyaye zaman lafiya na Amison suka kori Al Shebab da ke yakar gwamnati daga Mogadishiu. Sai dai har yanzu tana rike da yankuna da dama na  karkara, kana tana ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da na sojoji.