1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirkawa na zaben sabon shugaba

November 8, 2016

An fara kada kuri'a a zaben shugaban Amirka domin maye gurbin shugaba mai ci wato Barack Obama da ke barin gadon mulki

https://p.dw.com/p/2SLI1
Bildkombo Donald Trump und Hillary Clinton
Hoto: Reuters/C. Allegri/C. Barria

Tun da misalin karfe 5 agogon GMT ne dai aka fara kada kuri'a a wannan zabe kuma an soma shi ne daga jihar New Hamshire. Sassan kasar daban-daban za su fara zaben ne a lokuta daban-daban kasancewar Amirka na banbanci lokaci daga waje zuwa waje a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya rawaito cewar 'yar takarar jam'iyyar Demokrat a zaben Hillary Clinton ta kada kuri'arta a makarantar elementare a garin Chappaqua da ke New York kuma ta yi hakan ne tare da mijinta kana tsohon shugaban Amirka din wato Bill Clinton. Shi kuwa Donald Trump na jam'iyyar Republican da ke hamayya da Hillary ya zabi yin nasa zaben ne a Manhattan. Gabannin haka dai ya yi yunkurin karafafawa magoya bayansa gwiwa inda ya ce za su samu nasara a zaben lokacin da ya yi wani shiri ta kafafen watsa labarai da sanyin safiyar Talatar nan.

Kafin zaben dai, Amirkawa da dama sun maida hankali kan bin irin sharudan da hukumomi suka gindaya dangane da yadda za a yi zaben da ma irin matakan da suka kamata a bi wajen kada kuri'a. Za dai a rufe rumfunan zabe ne da maraice kana nan take za a fara kidayar kuri'a don fidda wanda ya yi nasara. A cikin watan Janairun da ke tafe ne dai za a rantsar da wanda ya samu galaba a zaben na Amirka wanda kuma shi ne zai maye gurbin shugaban kasar mai barin gado wato Barack Obama wanda shi ne bakar fata na farko a kasar da ya shugabanci Amirka.