1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Amurka na adawa da tsagaita wuta

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 8, 2023

Amurka ta ce tana adawa da matakin tsagaita wuta nan take, a rikicin yankin Zirin Gaza da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas na Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4ZxKF
Amurka | Majalisar Dinkin Duniya | Robert A. Wood
Mataimakin jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Robert A. WoodHoto: UN

Koda yake mataimakin jakadan kasar a majalisar Robert A. Wood ya ce Washington tana goyon bayan tsagaita wuta mai dorewa, sai dai ya bayyanawa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa ba sa goyon bayan ta afku cikin hanzari domin yin hakan a mahangarsu zai taimaki Hamas ne kawai. Kwamitin Sulhun dai, ya shirya taron ne domin kada kuri'a kan batun gaggauta tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza da nufin samun damar shigar da kayan agajin jin-kai.  Sai dai taron ya fuskanci tsaiko na tsawon sa'o'i, har sai bayan taron da aka shirya gudanarwa tsakanin ministocin kasashen Larabawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.