1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 9, 2024

Houthi dai ta sha alwashin ci gaba da kai hari kan jiragen ruwan da ke bi ta Baharmaliya, har sai Isra'ila ta dakatar da kai hari Gaza

https://p.dw.com/p/4dKep
Hoto: Osamah Yahya/ZUMA Press Wire via picture alliance

Amurka ta sanar da kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon Iran, kamar yadda shelkwatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar a Asabar din nan a shafinta na X.

Karin bayani:Iran ta yi allawadai da hare-haren da Amurka da Burtaniya suka kai Yemen

Harin ya fada ne kan makamai masu linzami da 'yan Houthi din suka girke a Juma'ar da ta gabata.

Haka zalika su ma 'yan tawayen Houthin sun mayar da martani ta hanyar harba makamai sau biyu zuwa gabar ruwan Aden, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito.

Karin bayani:Amirka ta lalata makaman 'yan Houthi a tekun Bahar Maliya

Ko da yake har zuwa wannan lokaci babu rahoton rasa rai ko jikkata sakamakon hare-haren guda biyu.

Houthi dai ta sha alwashin ci gaba da kai hari kan jiragen ruwan da ke bi ta Baharmaliya, har sai Isra'ila ta dakatar da kai hari Gaza.