1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An sako wasu da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza

Mahmud Yaya Azare M. Ahiwa
November 24, 2023

Yayin da aka fara musayar fursunoni tsakanin kungiyar Hamas da Isra,ila, ana ci gaba da neman a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki da safiyar Juma,a.

https://p.dw.com/p/4ZQWv
Gazastreifen Rotes-Kreuz Jeep in Rafah
Hoto: Ibraheem Abu Mustafa/REUTERS

Motocin daukar marasa lafiya na hukumar agaji ta Red Cross ne dai suka tsallaka iyakar Rafah ta Masar daga Zirin Gaza dauke da fararen hula 24 da Hamas ta kwashe makwanni bakwai tana garkuwa da su, bayan wani farmakin da ta kai cikin Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoba,ta hallaka sama da mutum 1,400. Wadanda aka sakan dai a yau Juma'a na daga yatsu da ke nuna alamar nasara. A yayin da ma'aikatan agaji ke musu tafi na kara karfafa gwiwa.

A yanzu an sauke su a wajen kula na musamman da aka tanada da ke da matukar tsaro, ana jiran isowar fursunonin falasdinawa da Isra'ila ta sanar da cewa, suna nan tafe kan hanya, kuma da sun iso wakilan falalsdinawa sun karbe su, an kammala matakin farko ke nan na musayen fursunonin.

Motocin Red Cross dauke da 'yan Isra'ila a Rafah
Motocin Red Cross dauke da 'yan Isra'ila a RafahHoto: MOHAMMED ABED/AFP

Isra'ila da Hamas dai sun cimma yarjejeniyar musayar mutum 50 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma tsagaita buɗe wuta na tsawon kwanaki hudu a yaƙin da suke yi.

Yarjejeniyar dai ta kunshi sakin falasdinawa 150 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila da kuma ƙaruwar taimakon jinƙai da za a shigar a zirin na Gaza, a madadin sako wadanda Isra'ila ke garkuwa da su su 50 din daki-daki cikin tsukin kwanaki hudun na tsagaita wuta.

Mai shiga Tsakani nakasar Qatar, Abdulmajeed Ridha ya ce duk da cewa an kira yarjejeniyar da tsagaita wuta, wato Hudnah, sai dai dukkanin kasashen duniya na fatan ganin ta rikide zuwa dauwammamen dakatar da bude wuta da sakin illahirin fursunonin da ke tsare a bangarorin biyu.

Shi kuwa Shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya matsa wa Isra'ila lamba ta aminta da cimma yarjejeniyar, cewa ya yi, ya yi amannar wannan yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen matsalolin da wadanda aka yi garkuwar da su ke fuskanta da kuma "rage raɗaɗin wahalhalun ga iyalan falasdinawa da ba su ji ba su gani ba."

Yadda ake murnar sako 'yan Isra'ila a birnin Tel Aviv
Yadda ake murnar sako 'yan Isra'ila a birnin Tel AvivHoto: Ariel Schalit/AP/picture alliance

Gwamnatin Isra'ila ta sha alwashin kammala yaƙinta na kawar da kungiyar Hamas tare da ceto sauran sama da mutane 200 da ƴan bindigar Hamas suka yi garkuwa da su a wani harin wuce gona da iri kan kudancin Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoba da Hamas ta kai, inda aka kashe mutane sama da 1,400.

Kungiyar Hamas, wadda Isra'ila da Amurka da Jamus da Tarayyar Turai da wasu sauran kasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin kungiyar ƴan ta'adda, ta ce yarjejeniyar za ta bai wa falasdinawa lokacin farfadowa bayan kazaman hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da ta kasa da  a Gaza, hare-haren da ta ce sun yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 14,500.