1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta tabbatar da zaben Mutfwang a Filato

Abdullahi Maidawa Kurgwi ZMA
September 22, 2023

Kotun sauraren kararakin zabe a Filato ta tabbatar da zaben Caleb Mutfwang na jama’iyyar PDP matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jiha.

https://p.dw.com/p/4Whbu
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A  zaman  shari'ar da  kotun tayi a wannan Juma'ar a jos,  alkalan kotun  sun yi watsi da  korafi  da  dan takarar  jam'iyyar  APC  Dr.

Nentawe  Yilwatda  yayi, wadda a cikinta ya ce, gwamna Mutfwang bai  cancanci  tsayawa takara ba a jam'iyyarMatsaloli kan zaben Najeriya PDP, kamar yadda tsohon sakataren jam'iyyar a jihar, Bashir Musan Sati ya shaida wa tashar DW.

An dai dauki tsauraran matakan tsaro a lokacin zaman shari'ar a birnin na Jos fadar jihar Plateau.