1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kokawa da tsadar takara a jam'iyyar APC

April 21, 2022

Kungiyoyi masu yaki da cin hanci da rashawa da matasa da sauran ‘yan siyasa sun fara mayar da martani kan yadda jam'iyyar APC mai mulki ta tsawwala kudin neman takara.

https://p.dw.com/p/4ADwl
Arfika Nigeria APC Abuja
Hoto: Ubale Musa/DW

Ana iya cewa zabukan Najeriya na shekara ta 2023 da ake tunkara sun zo da sabbin salo da kuma ba za ta ganin yadda manyan jama'iyyun da ke kan gaba wajen takara su ka ayyana kudaden sayen takardun neman tsayawa takara. Kudaden da jam'iyyar APC mai mulki ta ayyana shi ne ya fi ba da mamaki inda mai neman takarar shugaban kasa sai ya tanadi Naira miliyan 100, sabanin na jam'iyyar PDP da ta sa Naira miliyan 40 ko jam'iyyar NNPP mai kayan marmari Naira miliyan 30.

Kudin takarar gwamna da Sanata da na majalisar wakilai har ma da na ‘yan majalisun jihohi ma wanda jam'iyyar APC ta sa, ya ninka na sauran jam'iyyun da ke adawa. Tuni dai wannan matakin ya soma tayar da jijiyoyin wuya tsakanin ‘yan Najeriya da su ke ganin tsawwala kudaden ka iya zama tarnaki ko takunkumi ga dimukuradiyyar kasar.

Nigeria Vizepräsident Yemi Osinbajo (L)
Hoto: Press Office Yemi Osinbajo

A cewar kungiyoyin yaki da cin hanci wannan mataki zai bude sabbin kofofi ne na cin hanci tsakanin wadanda suka kashe wadannan makudan kudade domin tsayawa takara. Su kuma kungiyoyin matasa damuwa suka yi na cewa yawan kudin zai hana matasa da dama tsayawa takara tare da kuma karfafa siyasar uban gida duk da cewa an rage musu kashi 50% na kudin da za su biya.

Wasu daga cikin matasa ‘yan takara a jam'iyyar APC kamar Honorabul Ahmad Arabi Abul-Fathi, sun ce tsawwala kudaden barazana ce ga ‘yan takara da dama. ‘Yan Jam'iyyar APC da dama sun nemi shugabanninsu na kasa su sake tunani su rage farashin takardun neman takarar saboda mutane da da dama su iya shiga takarar, ta haka ne kawai za a karfafa dimukuradiyya jam'iyyar kuma ta kara karfi a idanuwan talakawa.