1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana yaba wa Tinubu da sauya hafsoshin tsaro

June 20, 2023

Al’ummar arewa maso gabashin Najeriya na martani kan sauyin manyan hafsoshin tsaro inda suke cike da fatan samun saukin rashin tsaro da aka kwashe shekaru ana fama da shi.

https://p.dw.com/p/4SqoS
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Da ma dai an yi hasashen samun wannan sauyi a kusan dukkanin fannonin tsaro na Najeriya saboda yadda aka kagu da samun saukin matsalolin tsaro da suka addabi sassan kasar. Bisa wannan ne ma ya sa daukacin al’ummar kasar ba su yi mamakin samun wannan sauyi na hafsoshin tsaro da Shugaba Sanata Ahmad Bola Tinubu ya yi ba.

Talakawan yankin arewa maso gabashin Najeriya da suka kwashe shekaru 14 suna fama da matsalolin tsaro karkashin gwamnatocin daban-daban, sun yi fatan a wanann karon sabbin hafsoshin na tsaro za su yi aiki tukuru domin kawo karshen matsalolin tsaron a yankin da sauran sassan Najeriya. Ali Rabkana Gashua na kungiyar muryar Talaka ta kasa, na daga cikin masu kallon abun a hakan.

Al’umma na bayyana cewa mutanen da aka nada dai kwararru ne kuma sun nuna bajintarsu a yaki da ta’addanci musamman sabon babban hafsan tsaro Manjo Janar Chris Musa wanda shi ne sila na mika wuya da dubban mayakan Boko Haram suka yi.

Sabi’u Alhaji Inuwa wanda aka fi sani da Malam Malam wani dan jarida ne da ya yi aiki da wasu daga cikin manyan hafsoshin tsaro yayin da suke aiki a shiyar arewa maso gabashin Najeriya. Shi ma ya yaba ayyukansu a baya.

Nigerianischer Soldat
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP

Sai dai akwai wasu kamar Badiya Sani Ya’u da ke ganin ya kamata ‘yan Najeriya su ba su goyon baya, ita kuma gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samar musu da kayan aiki da suke bukata domin su samu nasara.

Dukkanin alamu dai sun nuna cewa sauyin da aka na manyan hafsoshin tsaro na Najeriya da aka samu ya na yi wa al’ummar shiyar arewa maso gabashin kasar dadi saboda kwarin gwiwar da suke da shi na samun saukin matsalolin tsaro.