1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Annalena Baerbock ta ziyarci Gabas ta Tsakiya

November 12, 2023

Babbar jami'ar diflomaisyyar kasar Jamus, Annalena Baerbock ta ziyarci yankin falasdinawa da kuma Isra'ila. Yankuna ne da rikici da rikici ya sake kazancewa a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/4YixK
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena BaerbockHoto: Joseph Campbell/REUTERS

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ziyarci yankin Gabas ta Tsakiya, inda da farko ta gana da firamanistan yankin Falasdinu, Mohammad Shtayyeh a birnin Ramallah da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Daga nan kuma Baerbock ta isa birnin Tel Aviv na Isra'ila, inda ta tattauna da ministan harkokin wajen kasar, Eli Cohen.

Yayin wani taron 'yan jarida, babbar jami'ar diflomasiyyar ta Jamus ta tabbatar wa Isra'ila samun cikakken goyon bayan kasar Jamus.

Sai dai ta kuma bayyana cewa lallai ne kowace kasa ta tabbatar da bin dokokin kasa-da-kasa da suka shafi jinkan bil Adama.

Haka ma Annalena Baerbock ta yi kiran a rika bambanta fararen hula da wuraren da za a yi wa luguden bama-bamai.