1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Biden ya lashe zaben fidda gwani a Karolina ta Kudu

February 4, 2024

Shugaba Joe Biden ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat da aka gudanar a Karolina ta Kudu, abin da ke zama gwaji na farko ga shugaban a kokarinsa na neman wa'adin mulki na biyu a fadar White House.

https://p.dw.com/p/4c1T5
USA | US Präsident Joe Biden
Hoto: Matt Rourke/AP/picture alliance

Shugaban mai shekaru 81 a duniya ya yi wa abokan fafatawarsa guda biyu gagarumar zarra, inda ya tashi da kashi 96,4 cikin dari na kuri'un da aka kada. Abokan karawar tasa wadanda dukanninsu ba sanannu ba ne a fegen siyasar Amurka da suka hadar da Dean Phillips attajiri kuma shugaban wani kamfani na Ice Crem da marubuciya Marianne Williamson su kuma sun tashi da kashi biyu da doriya cikin dari.

Karin bayani: Zaben Amirka: Trump ya sha alwashin tuhumar Biden

Jim kadan bayan fitar da sakamakon zaben fidda gwanin, an hasko shugaba Joe Biden a hedikwatar yakin neman zabensa da ke jiharsa ta Delaware, yana aika sakon godiya ga magoya bayansa tare da shan alwashin zai doke Donald Trump da ake hasashen zai kasance mai kalubalantarsa a zaben shugaban kasar ta Amurka da za a gudanar a wantan Nowamba mai zuwa.