1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta sallami jakadan Jamus da ke kasarta

Ahmed Salisu
April 8, 2023

Rahotanni daga Ndjamenan kasar Chadi na cewar, gwamnatin soji kasar ta umarci jakadan kasar Jamus da ya bar kasar na nan da kwanaki biyu.

https://p.dw.com/p/4PpzT
Botschafter Gordon Kricke
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Rahotanni daga Ndjamenan kasar Chadi na cewar, gwamnatin mulkin soji kasar ta umurci jakadan kasar Jamus, Jan Christian Gordon Kricher, da ya bar kasar na nan da kwanaki biyu.

A wata sanarwa da suka fidda ta bakin kakakin gwamnatin kasar, hukumomin na Chadi sun ce sun yake shawarar korar jakadan na Jamus ne saboda ba ya mutunta dokokin diflomasiyya sannan mutum ne da ke yin katsalanda ga harkokin cikin gida na kasar.

Wakilin DW a birnin Ndjemena na kasar ta Chadi Abdulrazk Garba Babani ya rawaito ce ya zuwa yanzu jakadan bai kai ga mayar da martani kan wannan batu ba don kawo wannan lokacin ba wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar ya fidda kana ba wata sanarwa da aka samu daga ma'aikatar harkokin wajen Jamus din. 

Gabannin wannan sallama da aka yi wa jakadan dai, ya sha sukar hukumomin kasar kan jinkirta gudanar da zaben shugaban kasa da kokarin da ake yi na share wa shugaban da ke rikon kwarya, Mahmad Idriss Deby, hanya ta nema shugabancin kasar.