1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi ta waiwayi wadanda Hissene Habre ya azabtar

March 6, 2024

Hukumomin Chadi sun fara biyan diyya ga rukunin farko na kimanin mutum 10,000 da tsohon shugaban kasar Hissene Habre ya azabtar da su a lokacin mulkinsa na kama-karya.

https://p.dw.com/p/4dD20
 Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre yayin da ya gurfana a kotun a birnin Dakar
Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre yayin da ya gurfana a kotu a birnin Dakar Hoto: epa/dpa/picture alliance

Wata kungiya mai zaman kanta ce ta sanar da hakan inda ta ce kudin da za a ba wa mutanen ya kai akalla dala milyan 16 da dubu 500.

Habre da ake yiwa lakabi da ''Pinochet na Afrika", ya fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai  2017 a kotun hukunta laifukan yaki ta musamman sakamakon rawar da ya taka wajen keta hakkin 'dan adam, da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 40 a lokacin mulkinsa a Chadi.

Hissene Habre
Hissene Habre Hoto: AFP/Getty Images

Karin bayani:An sallami Hissene Habre daga kurkuku 

Shugaban hukumar kare hakkin 'dan adam na kasar ta Chadi Djidda Oumar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa akwai mutanen da lamarin ya shafa kimanin 10,800 da kowannensu zai samu CFA 925,000 kwatankwacin dalar Amurka $1,529.

Karin bayani: Chadi: Wadanda aka azabtar sun koka da rashin diyya

Hissene Habre ya mulki kasar ta Chadi tun daga 1982 har zuwa lokacin da Marigayi Idris Deby Itno ya hambarar da gwamnatinsa a 1990, inda zakara ya ba shi sa a ya tsallaka kasar waje.