1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina na kira da a tsagaita wuta a Ukraine

February 24, 2023

Kasar Chaina ta yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su hau teburin tattaunawa don sasanta rikicin da suka shafe shekara guda suna yi a maimakon ci gaba da amfani da makamai.

https://p.dw.com/p/4NwM2
Sojojin Ukraine sun yi shuru na minti daya a ranar cika shekaru guda da fara yakiHoto: Ukrainian Presidency/AP/picture alliance

A cikin wani kundi mai shafuka 12 da ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta wallafa a game da yakin Ukraine, ta yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta shiga tsakanin kasashen biyu domin sasanta rikicin cikin ruwan sanyi . Sannan ta soki barazanar yin amfani da makaman kare dangi a yakin  bayan shekaru guda da fara yaki, inda ta ce kawo yanzu babu wasu alamu na tsagaita wuta.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bakin jakadanta da ke Chaina Jorge Toledo ta ce za ta nazarci kundin tare kuma ta bayyana irin rawar da Chaina ya kamata ta taka wajen ganin a mutunta dokokin Majalisar Dinkin Duniya kan aikata laifukan yaki da kuma shinfida zaman lafiya.    

Sai dai shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier bayyana shakkunsa a game da matsayar ta Chaina a kan rikicin, yayin da shi kuma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya nuna gamsuwa tare da jinjina wa fadar Beijing kan kokarin da ta fara yi a baya-bayan nan na sasanta rikincin tare kuma da bayyana fatansa na yin zama na musanman da mahukunta Chainar domin kara tattaunawa a kan batun yakin.