1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban taƙaddama tsakanin Nijar da AREVA

Zainab MohammedFebruary 5, 2014

Kamfanin AREVA na Faransa mai aikin haƙo ma'addanai a Nijar ya dage cewar ba zai ƙara kuɗaɗen harajin da ya ke zuba wa ƙasar ba.

https://p.dw.com/p/1B3MN
Niger Uranabbau
Hoto: Getty Images

Kamfanin Dilancin Labarai na Reuters ya bayyana wani rahoto na hulda tsakanin kamfanin ƙasar Faransa mai aikin haƙo ma'addanai wato AREVA da kuma gwamnatin Nijar. Wanda har yanzu ta ke yin ƙasa ta na dabo a kan maganar ƙulla wata sabuwar yarjejeniya ta kwangilar aikin bayan da waccan ta kawo ƙarshen wa'adinta a cikin watan jiya. A ƙasa da shekaru 40 ƙasar Nijar ta zama ƙasa ta huɗu mai arzikin ma'addanan ƙarfen uranium wanda kuma tun lokacin ƙasar ke zaman jiran tsamani na samun canji na rayuwar al'ummar wadda sama da kishi 60 cikin ɗari na yawan al'ummar miliyan 17 ke yin rayuwa da ƙasa da dala Amirka ɗaya a yini.

Ƙishi biyu bisa uku na wutar lantarkin Faransa na dogaro da uranium na Nijar

Kusan kishi 40 cikin ɗari na ma'addanan na ƙarfen uranium da ake tonowa a Nijar na zuwa ƙasar Faransa ne wanda kuma kishi biyu bisa uku na wutar lantarki da ƙasar ke yin amfanin da shi ya dogara ne da uranium ɗin na Nijar.Tun a cikin watan Mayu na shekara bara ne dai aka soma yin tattaunawar tsakanin gwamnatin Nijar da AREVA da nufin samun daidaituwar baki domin cimma wata sabuwar yarjejeniya aikin haƙo ma'addanan musammun ma dangane da sabuwar rijiyar da za a fara aikinta a IMOURAREN da ke a arewacin na Nijar a shekarun 2015. Gwamnatin Nijar dai tana son kamfanin na AREVA ya ƙara kuɗaɗen harajin da ya ke biya ga ƙasar daga kishi biyar cikin ɗari zuwa kishi 12. Bugu da ƙari ma ministan haƙo ma'addanai na ƙasar ta Nijar Omar Hamidou Tchiana a wata tattaunawar da aka yi da shi ya ce ɓurinsu a nan gaba shi ne su kai aƙalla kishi 20 cikin ɗari na rarrar kuɗaɗen da za a samu daga ƙarfen.

Französische Geiseln zurück in Paris
Hoto: Reuters

AREVA na ƙorafin cewar kasuwar uranium ta faɗi

Sai dai kuma kamfanin na AREVA na ƙorafin cewar kasuwar uranium a duniya ta faɗi, amma kuma duk da haka alƙallumma da aka bayyana a farkon shekarun 2013 da kuma ƙarshen shekara kamfanin ya samu babbar riba wacce ta zarta kusan kishi 64 cikin ɗari na abin da ya saba samu. Marc Henri kakakin wata ƙungiyar da ke fafutuka rage makamashin nukiliya a duniya da ake kira da sunnan Sortie du Nucleaire ya ce a kwai yaudara da rainin wayo a cikin lamarin: '' Tsari ne da hakida irin ta mulkin mallaka wanda suke ganin har yanzu ƙasar ta Faransa tana da iko a kan wata ƙasar da ta yi wa mulki mallaka, abin da kamfanin ya ke yi wa Nijar kusan shekaru satin bai dace ba. Bayan sun ce ba su iya ƙara abin da suke bai wa Nijar ɗin a wani ɓangaran suna daɗaɗa wa wasu ƙasashen a kan aikin.'' Ba shakka a ƙasashen Kanada Kazakastan Australiya kamfanin na Areva na wannan aiki na haƙo ma'addanan ƙarfen uranium amma misali a Kazakhstan kamfanin na Faransa na zuba kusan kisha 18 cikin ɗari na kuɗaɗen da ya ke samu ga ƙasar.

NO FLASH Entführung im Niger
Hoto: AP

Al'ummar da ke zaune a yanki da ake haƙo uranium ɗin na cikin ƙunci

Wasu majiyoyin diflomasiya dai da aka tabbatar da gaskiyyar labarin da suka bayyana sun rawaito cewar Faransa ba a shirye ta ke ba ta ƙara yawan kuɗaɗen da ta ke bai wa Nijar. shin ko mi ke iya faruwa ganin cewar mai kaya ya dage ɓarawo ma ya dage Mar ya ce : '' A kwai ɗan ƙanƙanan alamu da ke nuna cewar za a iya samun sulhu tsakanin sassan biyu domin a yanzu kamfanin na AREVA ya koma aiki bayan da ya dakatar kan hujjar cewar suna yin gyare-gyare sai dai fa lamarin na da kamar wuya saboda kamfanin zai yi ƙoƙarin ƙara yin ƙasa ga abin da Nijar ta ke buƙata. Saboda a wani lokacin sun gaza samun kasuwa bayan hatsarin da ya faru na tashar nukiliya ta Fukushima kasuwar ƙarfen na uranium ta faɗi a duniya abin da ya sa a yau suke cikin halin matsi.Sannan kuma ga shi sha'anin Nukiliya na samun koma baya a duniya.''

Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

Kamfanonin dai guda biyu na AREVA a Nijar wato Somair da Cominak da ke da ma'aikata sama da dubbu biyu da ke yin aikin a garin Arlit da ke a yankin arewacin ƙasar, al'ummomin yankin na kokawa da su wajen rashin gina hanyoyin mota da makarantu da kuma samar da ababben more rayuwa. Saɓanin cikin wasu ƙasashe inda kamfanin ke yin aikin a Nijar jama'a da dama ne a arewacin ƙasar ke mutuwa a sakamakon cututtukan da ke da nasaba da shaƙar iska mai guba na ma'addanan abin da ke janyo zanga -zanga mazauna yankunan.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Yamai Mahaman Kanta ya aiko mana a kan martannin da ƙungiyoyin farAr hula da ama'a suka mayar a kan batun.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani