1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dabarun Biya na yaki da cin hanci a kamaru

Ramatu Garba Baba MAB
February 7, 2019

Kamaru na asarar biliyoyin kudi a duk shekara a sanadiyar cin hanci da rashawa duk da cewa shugaba Paul Biya ya kafa CONAC don yakar annobar. Wasu masana na sukar hukumar yayin da wasu ke sukar gwamnati kan gazawarta.

https://p.dw.com/p/3CwAh
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: imago/Xinhua Afrika

Hukumar da ke yaki da rashawa a Kamaru ta ce an dawo mata da kudaden da suka zarta biliyan dari uku da saba'in  na CFA. Manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministoci da shugabanin manyan masana'antu da na masana'antu da ke zaman kansu na daga cikin wadanda zargin cin hanci da rashawa ya dabaibaye. Ma'aikatar da ke kula da bayar da kwangilolin gwamnati ta kasance a sahun gaba daga cikin ma'aikatun da rashawa ta fi yi wa katutu, lamarin ya kai ga korar Abba Sadou, ministan da tuni ya sa kafa ya yi fatali da umarnin yana mai kalubalantar gwamnati

Titus Edzoa
Titus Edzoa na cikin manyan jami'an da ake samu da cin hanciHoto: GettyImages/AFP

Ya ce: "Mun dade muna yakar rashawa, don haka da wani minzani aka auna aka kai ga ayyana ma'aikatar a matsayin wace ta fi kowacce ma'aikata cin hanci. Ina son a sani cutar rashawa cuta ce da ta addabi kowa da ya kamata a yake ta a duk fannonin kasar.'' 

Wannan ya saka masu sa ido kan lamuran yau da kullum ke zargin wadannan ma'aikatu da aka samu da laifin aikata rashawa da kauce wa hanya, ganin yadda suke kokari na son tsame kansu daga duk wani zargi da ake musu.  AKo John malamin jami'a na ganin cewar kafa hukuma ba zai magance wannan annobar ba.
 
 Ya ce "Hukumar ta CONAC da ke yaki da rashawa ba ta yi nasarar magance matsalar ba, maimakon hakan ta kasance matattarar da matsalar cin hanci ta kama wuri ta zauna. Cin hanci ya kasance tamkar dafi mai illa ga ma'aikatu ganin yadda matsalar ta hanasu gudanar da duk wasu ayyuka na raya kasa''

FBL-CAMEROON-CAF
Cin hanci ya shafi kwallon kafa a KamaruHoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

 A fannin 'yan kasa kuwa, ba su mance ba da damar karbar bakuncin gasar cin kwallon kafa ta Afirka da ta subuce musu ba a sanadiyar takaddama ta rashawa. Su kuwa bangaren adawa sun zargi gwamnati ne da laifin sakaci a yaki da take da rashawa.  Barrister Ashu Agbor Emmanuel, na jam'iyyar adawa ta Reform, ya ce akwai bukatar a soma kawar da cin hanci da inganta rayuwar alkalan kotun kasar.

Ya ce: "Mu soma daga ma'aikatar shari'a, ya kamata a inganta rayuwarsu ta hanyar biyansu albashi mai tsoka."

Ba a rasa wadanda suke yabawa hukumar ta CONAC musanman yadda ta iya cakumo wasu da aka samu da laifi. Amma duk da haka akwai matsalolin da take ci gaba da fuskanta musanman kan gazawarta wajen hukunta wadanda aka samu da laifin cin hancin don kawai sun kasance manyan jami'an gwamnati.