1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amirka sun fara isa kasar Iraki

Mahmud Yaya Azare MAB
January 2, 2020

Amirka ta fara tura sojinta zuwa birnin Bagadaza duk da janyewar masu zanga-zangar adawa da ci gaban zaman Amirka a kasar Iraki, lamarin da ke jawo mai da martani daga 'yan kasar da ma makwabciyarta Iran.

https://p.dw.com/p/3VdIi
Das US-Militär bietet Sicherheit für das US-Botschaftsgelände in Bagdad nach Protesten
Hoto: picture-alliance/R. Gavaldon

Masu zanga-zanga sun nuna fushi dangane da hare-haren Amirka kan sansanonin mayakan Hezbulah ta Iraki, inda suka fashe-fashe a ofishin jakadancin Amirka d ake Bagdaza, kafin daga baya sun janye don amsa umarnin jagororinsu dama mahukuntan kasar.  Gidan talabijin Rasha na Russia Today  ya nuna wasu hotona da ya cena jakadan Amirka ne a yayin da yake tserewa daga ofishin jakadancin ta baya cikin tsauraran matakan tsaro.

USA Washington | Kapitol in Washington
Fadar Wahite House ta bada umurinin tura sojojin IrakiHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Cortez


  Amirka ta zargin Iran da tallafa wa mayakan na Hezbullah tare da marar hannu wajen kai farmaki ga ofishinta na jakadanci, kamar yadda kakakin fadar White House Mark Fessiner ke fadi. Ya ce: "Iran ta yi shigar burtu tana kan hare-hare kan ofishin jakadancinmu a Bagadaza. Muna kira ga mahukuntan Iraki da su gaggauta daukar matakan taka musu burki."

Tuni dai Amirka wacce ta ce harin da ta kai kan Hezbullah somin tabi ne, ta jefa daruruwan dakarun sojin kundumbala  a farfajiyar ofishin jakadancinta da ke kasar ta Iraki, wadanda za su share fagen tura karin wasu dakarunta da ake hasashen za su kai dubu biyu. Sai dai shugaban Addini na Iran Ali Khomeni ya musanta zargin Amirka na ingiza 'yan baranda don kai farmaki ga ofishin jakadancin Amirkan da ke Iraki,yana mai cewa, su ba matsorata ba ne, da za su buya a bayan katanga wajen tinkarar makiyansu.


 Junaid Haidary da ke ba wa shugaban Iran shawara ya ce: "Darasin da ya kamata Amirka ta fahimta shi ne, al'ummar Iraki ba ta kaunarta, ba ta kaunar ci gaba da zamanta a kasarsu. Mu kuma muna tayasu kan wannan kyaykyauwan halin. Ya rage wa Amirka ta fahimci haka ko kar ta fahimta."

Irak l  Proteste und Angriffe auf die US-Botschaft in Bagdad
'yan Iraki sun dakatar da zanga-zangar su a BagadazaHoto: picture-alliance/AP/K. Mohammed

 A nata bangaren gwamnatin Iraki ta ce a shirye take ta kare dukkanin ofisosin jakadancin kasahen ketare da ke kasarta, kuma tana ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amirka. Sai dai ta nemi Amirkan da ta dinga tuntubarta wajen aiwatar da duk wasu hare-haren da za ta dinga kaiwa a cikin kasarta. Sai dai  wasu yan majalisun Iraki sun sha alwashin ganin bayan duk wani yunkuri na dawowar sojin Amirka cikin Iraki.

A hannu guda kuma, masu zanga-zangar neman sauyi a dandalin Tahreer dake tsakiyar Bagadaza sun siffanta wannan dambaruwar da ke wakana a kasar da wani yunkuri na kawar da hankali 'yan kasar kan yunkurin neman sauyi da suka yi watanni suna yi a kasar.