1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Hamas da Isra'ila ya dauki sabon salo

October 7, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da harin makaman roka da kungiyar Hamas ta fara harba wa fararen hular Isra'ila, lamarin da ya sa shugaban kasar Ukraine ya ce ka da duniya ta zargi Isra'ila idan ta dauki mataki.

https://p.dw.com/p/4XFMj
Hoto: MOHAMMED SALEM/REUTERS

Mayakan Hamas sun ce suna tsare da gomman dakarun sojin Isra'ila a Zirin Gaza. Kakakin kungiyar, Abu Obeida ya ce sun kama jami'an ne a lokacin da suka kai samame kudancin Isra'ila a wannan Asabar din.

Tuni dai shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da yin Allah wadai da fadan da wannan sabon fada da ya barke a tsakanin Isra'ila da kuma kungiyar Hamas.

A martaninsa, shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya yi tir da harin da Hamas ta kaddamar yana mai cewa, Jamus na tare da kasar ta Isra'ila.

Tuni da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bukaci gaggauta kawo karshen rikicin yayin da Turkiyya ta bukaci bangarorin biyu da su mayar da wukakensu cikin kube. Wata majiya daga ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce, ministan da ke kula da ma'aikatar, Hakan Fidan, ya gana ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Katar da Saudiya da Masar da Palastine da kuma Iran domin tattauna hanyoyin tunkarar wannan rikici.