1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin EU ga tattalin arzikin Turai

Abdullahi Tanko Bala
April 10, 2020

Ministocin kudi na kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro sun amince da shirin gaggawa na ceto tattalin arzikin nahiyar Turai daga durkushewa sakamakon cutar coronavirus

https://p.dw.com/p/3ajwk
Kroatien Treffen EU-Außenminister in Zagreb
Hoto: Getty Images/AFP/D. Sencar

Ministocin sun cimma yarjejeniyar amincewa da tsabar kudi euro biliyan 500 domin tallafawa kasashen bayan tsawon makonni suna tattaunawa kan illar da annobar cutar coronavirus ta yi ga tattalin arzikin kasashen.

Shugaban rukunin kasashen masu amfani da kudin na Euro Mario Centano yace daukar matakin cikin hanzari ya zama wajibi idan aka yi la'akari da irin halin da aka shiga a baya shekaru goma da suka wuce lokacin da kasashen duniya ciki har da nahiyar turai suka fuskanci koma bayan tattalin arziki.

"Yace wannan shirin agajin gaggawar zai bada kariya ga tattalin arzikinmu da sha'anin jin dadin jama'armu da kuma walwalarsu yayin da muka fuskanci koma bayan tattalin arziki. Idan matsalar da ake ciki ta lafiya kau, za mu bukaci farfadowar tattalin arziki a saboda haka yana da muhimmanci mu hada kai mu cigaba baki daya."