1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaItaliya

Fafaroma ya yi kiran a samar da gajin jinkai a Zirin Gaza

October 15, 2023

Shugaban darikar Katholika na duniya, ya jaddada bukatar kai tallafi a Zirin Gaza, inda yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ke kara kazanta.

https://p.dw.com/p/4XYgZ
Jagoran darikar Katholika, Fafaroma Francis
Jagoran darikar Katholika, Fafaroma FrancisHoto: Marco Bertorello/AFP

Jagoran darikar Katholika na duniya, Fafaroma Francis ya yi kiran da a tsara hanyar da za a bi wajen tallafa wa al'ummar yankin Zirin Gaza na Falasdinu, inda Isra'ila ta mamaye a rikicin da ya barke tsakaninsu.

Fafaroma ya kuma jaddada kiransa a kan kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai da ta saki Isra'ilawan da ta kame tana garkuwa da su.

Fafaroma ya yi wannan kiran ne yayin jawabinsa na mako-mako ga dimbin mabiya a dandalin St. Peters, yana mai cewa bai kamata rikicin ya shafi kananan yara da marasa lafiya da mata da sauran fararen hula ba.

Jagoran da Katholika a duniya Fafaroma Francis, ya kuma ce wajibi ne a kula da hakkin samar da agajin jinkai, musamman a yankin na Zirin Gaza a halin da ake ciki.