1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauya fasalin bayar da bashi a duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
June 22, 2023

Wakilai daga kasashe sama da 100 na duniya da cibiyoyin da ke ta'ammali da kudi suna tattaunawa a birnin Paris na kasar Faransa, domin samar da sabon tsarin hada-hadar kudi na hadin gwiwa.

https://p.dw.com/p/4SwcC
Frankreich Gipfel des neuen globalen Finanzpakts in Paris
Shugaba Macron ne ya gayyaci sauran shugabannin duniya a taro kan tsarin lamuniHoto: Ludovic Marin/REUTERS

Shugaban Emmanuel Macron da ke daukar bakuncin taron ya ce wannan yunkurin zai ba da damar samun ci gaba a yakin da duniya ke yi da talauci da kuma shawo kan matsalar sauyin yanayi. Burin da Macron ya sa a gaba, shi ne gaggauta yin garambawul ga tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa, wanda ya samo asali daga yarjejeniyar Bretton Woods a 1944 wadcce ta bada damar kirkiro da IMF da bankin duniya.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da firaministan kasar Sin Li Qiang na daga cikin mahalarta zaman da za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa. Dama dai Sin, na daya daga cikin manyan kasashen duniya masu ba da lamuni da ake yawan zargi da rashin shiga cikin tsarin sake fasalin bai daya na hada-hadar kudi tare da kasashen yammacin duniya.