1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fasahar AI na barazana ga rayuwar dan Adam

Abdullahi Tanko Bala
May 30, 2023

Masana kimiyya da shugabannin kamfanonin fasaha da suka hada da Microsoft da Google sun yi kashedi game da hadarin fasahar Artificial Intelligence na mutum mutumi mai kaifin basirar dan Adam ga rayuwar bil Adama

https://p.dw.com/p/4Rz0z
Künstlerische Darstellung eines humanoiden Roboters mit künstlicher Intelligenz
Hoto: Knut Niehus/CHROMORANGE/picture alliance

A cikin wata sanarwa da suka fitar masana kimiiyya sun yi gargadin cewa magance barazanar Artificial Intelligence na mutum mutumi mai kaifin basirar dan Adam lamari ne da ya kamata duniya ta mayar da hankali akai da kuma wasu kalubalen da suka addabi al'umma kamar annoba da kuma yaki da makaman kare dangi.

Sam Altman shugaban kamfanin ChatGPT wanda ya samar da OpenAI da Geoffrey Hinton masanin kimiyyar Kwamfuta da aka fi sani da jigon fasahar Artificial Intelligence mai kaifin basira irin ta dan Adam, suna daga cikin daruruwan fitattun mutane da suka sanya hannu a kan sanarwar da aka wallafa a shafin cibiyar kariya ta fasahar Artificial Intelligence.

Damuwa kan cewa fasahar Artificial Intelligence na iya shafe tasirin dan Adam ta karu yayin da aka sami karuwar sabbin nau'in fasaha irin ChatGPT wanda ya sanya kasashe bazama wajen tunanin yadda za a samar da dokoki domin takaita cigaban fasahar.

.