1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Barrow zai sake takara a Gambiya

June 15, 2023

Al'ummar kasar Gambiya da dama na bayyana takaicinsu a kan sanarwar da Shugaba Adama Barrow ya yi ta cewa zai sake tsayawa takara, duk da a baya ya yi alkawarin mika mulki bayan shekaru uku kacal.

https://p.dw.com/p/4SbLH
Gambiya l Shugaban Kasa | Adama Barrow
Shugaba Adama Barrow na GambiyaHoto: Leo Correa/AP/picture alliance

Shugaba Adama Barrow wanda kafin yanzu ya yi alkawarin mika ragama ga wata zababbiyar gwamnati bayan mulkin shekaru uku kacal, ga dukkan alamu ya kama hanyar zama kan karaga kamar yadda wanda ya gada tsohon Shugaban kasar  Yahya Jammeh ya yi. Ya kuma bayyana wannan aniyar tasa a yayin wata ganawa da ya yi da masu goyon bayansa a yankin Central River na kasar a baya-bayan nan. Yanki ne dai da jam'iyyarsa ta National People's Party NPP ke da rinjayen magoya baya. Sai dai masu sukar lamirin Shugaba Barrow na cewa, ya kamata ya yi amfani da wa'adinsa da ya saura wajen inganta rayuwar talakawa maimakon maganar sake takara a karo na uku.

Gambiya | Zanga-Zanga | Adawa | Shugaba Kasa | Adama Barrow
A shekara ta 2019 dai, an gudanar da zanga-zangar bukatar Baroow ya ajiye mulkiHoto: DW/O. Wally

Tsarin mulkin  kasar ta Gmabiya dai, bai iyakance yawan wa'adi da shugaban kasa zai iya yi yana mulki ba. Duk da cewa shugaban mai ci Adama Barrow mai shekaru 57 ya ce zai mika mulki ga wata gwamnatin bayan shekaru uku, yana kuma da 'yanci a dokance ya nemi karin wa'adin. Sai dai wani malami a sashen nazarin ilimin kimiyyar siyasa a jami'ar Gambiyan Essa Njie na da ra'ayin cewa, Shugaba Barrow na amfani ne da mafita da kundin tsarin mulki ya bayar ba bisa tsari ba. Karamar kasar ta yankin yammacin Afirka wato Gambiya da kuma ke da yawan al'umma miliyan biyu da dubu 600, kasa ce da shugabanni uku kacal suka mulke ta tun bayan samun 'yancin kai a farkon shekarar 1965. Tsohon Shugaba Yahya Jammeh wanda mulkinsa ya kawo karshe a ranar 21 ga watan Janairun 2017 ne ya fi dadewa yana mulki a Gambiya, bayan da ya kwashe shekaru 33.