1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kokarin tsagaita wuta a yankin Zirin Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 6, 2024

Kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu, ta sanar da mika amsoshinta dangane da batun tattauna yiwuwar tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/4c6xV
Isra'ila | Tel Aviv | Zanga-Zanga | Adawa | Yaki
Zanga-zanagr adawa da yakin Zirin Gaza a Isra'ilaHoto: AHMAD GHARABLI/AFP/Getty Images

Ana fatan yarjejeniyar tsagaita wutar da kasashen Masar da Qatar suke shiga tsakani, za ta bayar da damar sakin sauran wadanda kungiyar Hamas din ke garkuwa da su tun bayan harin ba-zata da ta kai Isra'ila a watan Oktobar bara. Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya tabbatar da cewa kasarsa na yin nazarin amsar da kungiyar ta Hamas ta bayar da kuma fatan za a samu tsagaita wuta mai dogon zango, domin sakin baki dayan sauran mutanen da Hamas din ke ci gaba da yin garkuwa da su.