1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gazawar tsarin dimukuradiyya a Afirka

Uwais Abubakar Idris
April 12, 2024

Wani nazari da cibiyar nazarin dimukurdiyya da harkokin zabe ta gudanar ya gano yadda jama’a ke jan baya da tsarin dimukurdiyya saboda gazawar da tsarin ke yi wajen biya musu bukatu.

https://p.dw.com/p/4ei3N
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Wani nazari da cibiyar nazarin dimukurdiyya da harkokin zabe ta gudanar ya gano yadda jama'a ke ja baya da tsarin dimukurdiyya saboda gazawar da tsarin ke yi wajen biya masu bukata. Wannan ya sanya jama'a na nuna hali ko in kula da bin tafarkin mulki na kama karya maimakon dmukurdiyya. Shin ke haifar da wannan ne kuma mene ne hatsarin da zai iya haifarwa.

Binciken dai cibiyar ta gudanar a tsanake a kan wannan batu na tafarkin mulkin dimukurdiyya, tasirinsa da ma yadda jama'a ke kalonsa a yanzu, inda a kasashen 19 da cibiyar nazarin dimukurdiyya da harkokin zabe tya Idea ta gano cewa sannu a hankali fatan da jama'a ke da ita a kan mulkin dimukurdiyya na raguwa sosai. Wannan na faruwa kama daga kasashen da suka ci gaba da sune suka yanke wa tsarin cibiya ya zuwa nba Afrika da suka ara suka yafa.

Guguwar sauyi da take kadawa a kan yadda ake tafiyar da dimukurdiyya musamman a bangaren ‘yan siyasar kansu shine abin dubawa, domin kasashen da dama sun yi watsi da tsarin da aka san su da shin a siyasa da ma mulkin dimukuridyyar. 

Abin da yafi daga hankali a sdakamakon binciken da cibiyar ta Idea ta gudanar ya gano shine yadda hallayen mutane ke chanzawa daga tafarkin mulki da ya basu daman zaben shugabanin da zasu jagorancin al'ammuransu ya zuwa masu kama karya. Domin zabi na siyasa da dimukurdiyya ya samar bai dadasu da kasa ba a yanzu, sun ma fi son tafarkin mulzki ban a dimukurdiyya ba ko dai na mulukiyya ko kama karya. 

Duk da wannan hali da ma barazana da ke fusknatar tsarin dimukurdiyya a yanzu binciken ya nuna a kasashe 11 cikin 19 alumma sun nuna gamuswa da tsarin zabe, amma kuma a kasha takwas jama'a sun nuna sha'awar samun shugaba mai tasiri ba wai dole sai ta hanyar zabe ba.

To sai dai duk da wannan cikas da tafarkin dimukurdiyya ke fusknata ga Farfesa Jibo Ibrahim manazarci a cibiyar nazarin dimukurdiyya da ci gaban kasa ya bayyana cewa tsarin ya yi nuna juriya da jajaircewa kuma koma bayan da ake fuskanta na faruwa nje saboda raunin cibiyoyi kula da dimukurdiyyar.