1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gidauniyar Jamus ta karrama matan Kamaru

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim M. Ahiwa
December 1, 2023

idauniyar Jamus ta karrama wasu mata uku da suka yi fice wajen kare hakkin mata a Kamaru da lambar yabo ta bana. Matan sun yi suna a bangaren raya dimukuradiyya da al'adu d.s.

https://p.dw.com/p/4ZgSZ
Yadda gidauniyar Jamus ta karrama matan Kamaru a birnin Berlin
Hoto: Isaac Mugabi/DW

Matan da Jamus ta karrama su ne; Marthe Wandou da Esther Omam da kuma Sally Mboumien, wadanda mambobi ne na kungiyar nan ta 1st National Women's Convention for Peace in Cameroon, wadda ke aiki kafada-da-kafada da shirin bunkasa ci gaban matasa na DW wato 77 Percent. Mata ne da suka yi suna wajen raya ci gaban al'uma ta fuskar dimukuradiyya da al'adu da tattalin arziki da kimiyya, baya ga kare hakki.

Marthe Wandou wadda lauya ce, ta dukufa matuka a kauyen Makolo na arewacin kasar Kamaru, wajen ganin an bar yara suna zuwa makaranta, bayan tashin hankalin da kasar ta rinka fuskanta, tun daga lokacin da 'yan awaren kasar na Ambazoniya suka fara ta da kayar baya ta bukatar ballewa a shekarar 2017. Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu shida, tare da raba sama da dubu dari bakwai da gidajensu. Yayin da a gefe guda kuma 'yan Boko Haram ke kai hare-hare suna kashe mutane, tare da yin garkuwa da su suna yi wa mata fyade.

Kamerun Hilfsnetzwerk für Vergewaltigungsopfer
Hoto: Elisabeth Asen Somo/DW

A nata bangaren Esther Omam, wani asibitin sha ka tafi ta samar a Kauyen Debundscha da ke kudu maso yammacin Kamaru, karkashin gidauniyarta ta Reach Out Cameroon, wadda ta shafe sama da shekaru 20 tana agaza wa mutanen yankin, musamman ma wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, inda take bayar da magunguna kyauta da kuma shawarwari ga dubban marasa lafiyar da ke ziyartar ta a kowane mako.

A birnin Bamenda da ke arewa maso yammacin Kamaru kuwa, Sally Mboumein ta yi fice ne wajen gwagwarmayar kwato hakkokin matan da aka ci wa zarafi musamman ma fyade, kasancewar ita ma daga yankin ta fito. Inda take kula da lafiyarsu ta kuma ba su shawarwarin kyautata rayuwarsu ta gaba, bayan muzgunawar da suka fuskanta.

Sally Mboumein dai ta zama madubi abar koyi ga 'yan mata wajen samar da kyakkywan tsari na shugabanci da kuma zaman lafiya a kasar Kamaru.