1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa mai karfin maki 7,4 a Japan

November 22, 2016

Wata girgizar kasa da ta abku a wannan Talata a kasar Japan ta haddasa igiyar ruwan tsunami a kusa da tasoshin nukiliyar Fukushima wadanda suka yi hatsari a watan Maris na shekara ta 2011. 

https://p.dw.com/p/2T2nv
Japan Fukushima
Hoto: Reuters/T. Hanai

Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar ta Japan ta ce girgizar kasar mai karfin maki 7,4 a ma'aunin girgizar kasa na Richter ta wakana ne a karfe shida saura minti daya na kasar wato karfe tara saura minti daya na daran jiya agogon JMT. 

Kuma da misalin karfe shida da rabi na safiyar yau ne aka fuskanci igiyar ruwan tsunamin mai tsawon mita daya a wajen tashoshin nukiliyar guda biyu na Fukushima. Sai dai kuma kamfanin lantarki naTepco wanda ke kula da tashoshin nukiliyar guda ya ce kawo yanzu babu wata barazana da ko kuma wata illa da ta samu tashoshin nukiliyar a sakamakon girgizar.