1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 36 sun mutu a Brazil

February 20, 2023

Wata munmunar guguwa hade da ruwan sama mai karfi da ba a taba ganin irinsu ba sun yi ajalin mutane 36 a wasu birane biyar na yankin Sao Paulo a kasar Brazil.

https://p.dw.com/p/4Nj4V
Brasilien | Erdrutsch nach Starkregen in Petropolis | Suche nach Überlebenden
Hoto: Jose Lucena/TheNEWS2 via ZUMA Press Wire/Zumapress/picture alliance

A sanarwar da Mahukutan yankin suka fitar sun ce an fuskanci guguwar da ruwan saman ne a karshen wannan mako yayin da a ke bukukuwan Kanival, kuma ana sa ran nan zuwa gaba a sami karin adadin wadanda suka rasu. To sai an yi nasar canja wa mutane 228 matsauguni tare kuma ta kwashe karin wadansu mutane 338 bayan anyana dokar ta ba ce a birane biyar dake yankin.

Shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva ya kai ziyara gani da ido da kuma nuna alhini ga al'umma yankin bayan bayan aukuwa lamarin da kasar ba taba fuskantar irinsa ba.

Wannan dai shine karo na biyu a kasa da shekara guda da kasar Brazil ke fuskanta irin wannan ibtila'i da ke zama daya daga ababen da dumamar yanayi ke haddasawa, domin ko da a shekarar da ta gabata ruwan sama mai karfi ya yi ajalin mutane sama 230 a yankin Rio da Jenero.