1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila ta tsananta farmaki a kudancin Zirin Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou
January 20, 2024

Sojojin Isra'ila na kara matsa luguden wuta a yankunan kudancin Gaza, a daidai lokacin da hukumomin yankin ke cewa akwai tsananin bukatar a shigar da kayayakin agaji.

https://p.dw.com/p/4bUOo
Hoto: AFP/Getty Images

Ma'aikatar lafiyar Gaza na cewa sojojin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a Khan Younes da ke kudanci, yankin da Isra'ilar ke ikrari da cewa mabuyar 'yan Hamas ne. A tattaunawar da ya yi da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho, shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana goyon bayansa ga batun kafa wata kasar Palastinu, tare da kira ga Isra'ila da ta kiyaye rayukan fararen hulla. 

Karin Bayani:  An tsinke layin tarho da intanet a yankin zirin Gaza tsawon mako guda ,

Sai dai kakakin fadar White House John Kirby, ya ce Shugaba Biden ya bayyana cewa da akwai jan-aiki a gabanin kai ga gabar kafa wata kasar Falasdinawa. Ma'aikatar lafiyar Falasdinawa ta ce an kashe mutane fiye da dubu 24 da 700 galibi mata da kananan yara, tun bayan da Isra'ila ta kaddamar farmaki a Zirin Gaza a kokarinta na kakkabe mayakan Hamas.