1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Hukumar zabe ta tuhumi tsohon fraministan Pakistan

Zainab Mohammed Abubakar
January 3, 2024

Hukumar zaben Pakistan ta tuhumi Imran Khan da laifin raina hukumar, matakin da ya shafi zarge-zargen da ya yi na batanci ga babban kwamishinan zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4apSS
Imran Khan
Hoto: Mohsin Raza/REUTERS

Tsohon dan wasan Cricket din mai shekaru 71 Khanya shiga cikin rikicin siyasa da ta shari'a tun bayan da aka hambarar da shi a matsayin firaminista a watan Afrilun 2022.

Ba a dai sake ganin shi a bainar jama'a ba tun bayan da aka daure shi na tsawon shekaru uku a watan Agusta bisa laifin sayar da kayayyakin gwamnati ba bisa ka'ida ba, a lokacin da yake kan mulki daga 2018 zuwa 2022.

Lauyan shi Haider Panjutha, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewar,humumar zabenkasar ta yanke wa Imran Khan hukunci ne ba tare da bayyanan lauyoyinsa ba.