1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: ICC na binciken laifukan yaki

July 14, 2023

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC, ta sanar da bude sabon bincike dangane da zargin aikata laifukan yaki a Sudan.

https://p.dw.com/p/4TsUO
Babban mai gabatar da kara a kotun ICC, Karim Khan
Babban mai gabatar da kara a kotun ICC, Karim KhanHoto: Peter Dejong/AP/picture alliance

Babban mai gabatar da kara na kotun Karim Khan ne ya bayyana hakan a cikin rahoton da ya aike wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, watanni uku bayan barkewar rikici tsakanin bangarorin sojan kasar tare da nuna damuwarsa kan yadda rikici ke kara kamari a Sudan din da ke yankin Arewa maso Gabashin nahiyar Afirka. Khan ya kara da cewa, binciken nasu zai mayar da hankali ne a kan cin zarafi da fyade da kuma kai hare-hare kan fararen hula. Alkaluma sun yi nuni da cewa kimanin mutane dubu uku ne aka kashe yayin da wasu fiye da miliyan uku suka rasa matsugunnansu, tun bayan barkewar rikici tsakanin shugaban rundunar sojojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa kana shugaban mayakan RSF Mohammad Hamdan Daglo. Da ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar karin kisan kiyashi musamman a yankin Darfur. Tun dai a shekara ta 2005 ne ICC din ke bincike a yankin Darfur na Sudan, inda kotun a baya ta zargi tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir da aikata kisan kiyashi.