1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: martani kan bukatun IMF

February 13, 2024

Masana da masharhanta gami da talakawan yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, sun fara mayar da martani kan bukatar da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya mika ga gwamnatin tarayya.

https://p.dw.com/p/4cMga
Najeriya I IMF | Tallafi | Makamashin Lantarki
Tambarin Asusun ba da Lamuni na Duniya IMFHoto: Gripas Yuri/ABACA/IMAGO

Asusun na IMF dai ya shawarci Najeriya da ta janye tallafin da ake bayarwa kan makamashin wutar ne, kan dalilin cewa tana kashe abin da ya fi karfinta wanda hakan ke janyo matsala ga tattalin arzikin kasa. Asusun ba da Lamunin na Duniya IMF ya ce cire tallafi a fannin makamashin wuta da na man fetur zai taimakawa kasar wajen habaka tattalin arzikinta, saboda haka ya zama dole gwamnatin tarayya ta rufe ido ta cire tallafin. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar kasar ke shan ukuba ta matsatsin tattalin arzikin kasa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da ya haifar da yunwa tsakanin al'ummar kasar.

Najeriya I IMF | Tallafi | Makamashin Lantarki
'Yan Najeriya da dama dai, na fama da kuncin rayuwaHoto: DW/A.Kriesch

Amma masana da masharhanta kamar Dakta Murtala Abdullahi Kwara na jami'ar Umaru Musa 'Yar Adua da ke Katsina, na ganin bai kamata gwamnati Najeriya  ta bi wannan shawara a wannan lokaci ba saboda halin da al'umma ke ciki. A cewar Farfesa Lawal Jafar Tahir na jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu, ba su yi mamakin wannan matakin na IMF ba kuma talakawa ne za su kara fadawa halin ni tasku. Talakawan da cire tallafi mai yanzu haka ya ke gasawa aya a hannu dai, sun nemi gwamnatin tarayya da ta yi watsi da wannan shawara ta IMF. Ya zuwa yanzu dai Asusun na IMF ya samu shawo kan gwamnatin Najeriyar wajen cire tallafi a harkokin noma mumsamman kan takin zamani da kuma albarkatun man fetur, inda masana ke ganin cire tallafi a fanni makamashin wutar lantarki wacce da ma ba ta wadaci kasar ba ka iya bude sabon shafi da wahalhalu ga al'ummar kasar.