1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Najeriya da Cuba na son shiga BRICS

Abdul-raheem Hassan AH
August 23, 2023

Brics: Shugabannin kungiyar sun sha alwashin rage tasirin kasashen yammacin duniya bayan amincewa da bude kofar ga sauran kasashe don sake fasalta tsarin duniya.

https://p.dw.com/p/4VVxJ
Daga hagu zuwa dama Shugaban Kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da Xi Jinping na China da  Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da firaministan Indiya Narendra Modi da Sergei Lavrov jagoran diplomasiya na Rasha
Daga hagu zuwa dama Shugaban Kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da Xi Jinping na China da Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da firaministan Indiya Narendra Modi da Sergei Lavrov jagoran diplomasiya na Rasha.Hoto: Alet Pretorius/REUTERS

 Shugabannin kungiyar sun sha alwashin rage tasirin kasashen yammacin duniya bayan amincewa da bude kofar ga sauran kasashe don sake fasalta tsarin duniya. Taron Kiraye-kirayen kara fadada kungiyar BRICS, ya mamaye ajandar taron na kwanaki biyu da aka fara ranar Talata a binrin Johannesburg, sai dai yayin da Indiya da ke zama babar jigo a kungiyar, ta nuna shakku kan matakin daga wa sauran ksashen kofar shiga, China ta ce matakin shi ne mafi kyau na habakar  BRICS cikin sauri. Akalla shugabannin kasashen duniya 50 ne suka halarci taron Bricks na bana, tuni kusan kasashe goma sha biyu da ke wakiltar kaso 40 cikin 100 na akl'ummar duniya da kaso daya bisa hudu na tattalin arzikin duniya suka nuna sha'awar shiga kungiyar a hukumance. Kasashen BRICS sun hada da manya da kananan kasashe masu karfin tattalin arziki da dimokuradiyya da masu mulkin kama karya, wato Brazil da China da Rasha da Indiya da kuma Afirka ta Kudu, suna sha alwashin kalubalantar tsarin duniya da kasashen yamma ke jagoranta, wanda suka ce ba ya amfani da muradunsu ko kuma samun daukaka.

Vladmir Putin ya halarci taron ta bidiyo
Vladmir Putin ya halarci taron ta bidiyoHoto: Mikhail Klimenty/imago imsges

Tuni dai Amirka ta yi watsi da tafiyar BRICS, wacce ta kwatantanta da tarin kasashen da ke kunshe da abokai da abokan hamayya. Kasashen Afirka ta Kudu da China da Indiya ba su yi Allah-wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ba, yayin da Brazil ta yi watsi da matakin kasashen yammacin duniya wajen aika makamai zuwa Ukraine ko kuma sanya takunkumi kan Moscow.