1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ingantuwar dangantakar Rasha da Nijar

Salissou Boukari ZMA
April 12, 2024

Tawagar farko ta sojojin Rasha ta isa Jamhuriyar Nijar tare da tallafin wasu kayan yaki na zamani da Rashar ta bai wa kasar.

https://p.dw.com/p/4ei3p
Tutocin kasashen Nijar da Rasha
Tutocin kasashen Nijar da RashaHoto: AFP/Getty Images

Rasha ta aikewa Jamhuriyar Nijar makaman kakkabo jiragen yaki na sama da kuma kwararrun sojoji 100 da za su bai wa sojojin kasar horo na musamman kan dabarun yaki.

Gidan talabijin din gwamnatin Nijar na RTN ya ruwaito cewa a karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma ma'aikatar tsaron Rasha za ta girka na'urorin nadar bayanai a Nijar tare bayar da ingantaccen horo ga sojojin kasar don fuskantar ta'addanci. 

Karin bayani: Rasha ta aikewa Nijar makaman kakkabo jiragen yaki da sojoji

Hukumomin Nijar sun bayyana hakan a matsayin wani ci gaba da aka samu bayan tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Vladmir Putin na Rasha ya yi da takwaransa na Nijar Janar Abdourahamane Tiani a karshen watan Maris da ya gabata kan batutuwa da suka shafi karfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen kasashen biyu.

Shugaba Tiani na tattaunawa da Putin ta wayar tarho
Shugaba Tiani na tattaunawa da Putin ta wayar tarhoHoto: CNSP

Sai dai a daidai lokacin da wasu ‘yan Nijar ke bayyana farin cikinsu da zuwan sojojin Rashar a kasar ta Nijar, wasunsu na kira ga mahukuntan Nijar din da su yi taka tsan-tsan a wannan mu'amala da Rasha, domin kauce wa irin kura-kuran da Nijar din ta aikata a baya a fannin huldar soji da Faransa da Amurka wadanda ta raba gari da su a baya-bayan nan.

Karin bayani: Rasha ta samu karbuwa a Nijar

A lokacin da suka isa birnin Yamai a ranar 10 ga watan Afrilu, daya daga cikin tawagar sojojin na Rasha ya bayyana cewa: "Mun zo ne nan Nijar domin horas da sojojin kasar kan yadda za su sarrafa sabbin kayan yakin da kasarmu ta bai wa Nijar.''

Abin jira a gani a nan gaba shi ne tasirin da zuwan sojojin Rasha da ma tallafin kayan yakin na zamani ga yaki da ta'addanci da sauran matsalolin tsaro a kasar.