1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Jama'a na yin tir da hare-hare a Borno da Yobe

November 2, 2023

Mayakan Boko Haram da ISWAP sun farfado da hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro inda cikin kwanaki biyu suka halaka mutane da dama a Borno da Yobe. Sai dai hukumomi na cewa suna daukar matakan dakile hare-haren .

https://p.dw.com/p/4YKVO
Mutane da dama sun rasa rayukansu a sabbin hare-hare a jihohin Borno da Yobe
Mutane da dama sun rasa rayukansu a sabbin hare-hare a jihohin Borno da YobeHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Baya ga harin da Kungiyar ISWAP ta kai inda ta halaka mutane 40 a jihar Yobe wanda shi ne mafi muni a watanni 18, ita ma Kungiyar Boko Haram ta halaka wani limami da na'ibinsa gami da wani jami'in tsaro a Karamar hukumar Kaga ta jihar Borno. Haka kuma mayakan na Boko Haram  sun halaka wasu mutane a karamar hukumar Bama a jihar Borno tare da kame matafiya da dama a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, abn da aka kwashe kusan shekara guda ba a gani ba a wannan hanyar. Dawowar wadannan hare-hare sun dagulawa al'ummar wannan yankin lissafi bayan da suka fara sakin jiki, ganin cewa an samu zaman lafiya na tsawon lokaci.

Mutane na rasa muhallansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga
Mutane na rasa muhallansu sakamakon hare-haren 'yan bindigaHoto: Reuters/K. Adewale

 Idris Baffa Geidam, wani dan yankin da aka kai wadannan hare-hare a jihar Yobe ya bayyana cewa: " Akwai fargaba ga mutanen da suke zaune a kauyukan da ke karamar hukumar Geidam musamman ma gabashi da kudancin Geidam. Gaskiya mutanen da suke wadannan kauyuka na zaman fargaba da zullumi sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.”

Karin bayani:Hare-hare na illata sana'o'i a yankin tafkin Chadi

Shi kuma Ahmad Usaini ya nuna damuwa kan abin da ya faru saboda babu wasu hukumomi da suka kai musu tallafi ko makamantansu. A nasu bangaren, masana da masharhanta na na cewa ba su yi mamakin samun wadannan nan hare-hare a wannan lokaci ba saboda an saki jiki duk da cewa ba kare wannan yaki ba.

Jami'an tsaron Najeriya na daukan matakai don dakile matsalar tsaro
Jami'an tsaron Najeriya na daukan matakai don dakile matsalar tsaroHoto: Reuters/Reuters TV

Dr Lawal Jafar Tahir, Shehin malami a jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu ya ce: " Yaki ne na sunkuru kuma za a iya shammatar mutane a kowane lokaci. Wadannan yaran sun zauna a jejin nan ba wai sun bar wannan abin ba ne, saboda haka ya faru. Yawancin masana bai zo musu da mamaki ba saboda sun dade suna sharhi a kan cewa wannan bai kare ba, gara a sake daukar mataki..”

Karin bayani:'Yan Najeriya sun ce ba a murkushe ta'addanci ba

Jami'an tsaro sun ce suna daukar matakai da suka kamata na ganin an magance wadannan hare-hare da mayakan na Boko Haram ke kaiwa. Babban Hafsan tsaro na Najeriya Janar Christ Musa ya ce ya kamata mutane su bai wa jami'an tsaro hadin kai da ya kamata domin dorewar nasarar da aka sa a gaba. Yanzu haka dai an shaida ganin karuwar matakan tsaro a kan hanyoyin wannan shiyya  ganin cewar ana fuskantar matsala lokacin tafiye da kuma bukuwan karshen shekara.