1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Arangama da jami'an tsaro kan matakin dage zabe a Senegal

Binta Aliyu Zurmi
February 6, 2024

Jami'an tsaro a kasar Senegal sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga a kan matakin da majalisar kasar ta dauka na dake babban zaben kasar har zuwa karshen wannan shekara.

https://p.dw.com/p/4c5Ef
Senegal Dakar | Bereitschaftspolizei wirft Tränengas auf Opposition
Hoto: Stefan Kleinowitz/AP/picture alliance

A jiya Litinin ne 'yan majalisu 105 suka kada kuri'ar amincewa da kudirin yayin da wani dan majalisa daya ya nuna kin amincewarsa, bayan jami'an tsaro sun fitar da 'yan adawa daga cikin majalisar ta hanyar amfani da karfi.

Wannan mataki dai, na nufin share fage ga Shugaba Macky Sall da ke neman kasancewa a kan madafun iko har sai an samar da wanda zai gaje shi da ya amince da shi.

Wannan dai shi ne karon farko da kasar Senegal ke jinkirta zaben shugaban kasa, kuma tuni 'yan adawa suka yi watsi da matakin kai zaben watan Disamba tare da kiran magoya bayansu da su fito don nuna adawarsu. An katse kafar Intanet da ma dakatar da wata kafar yada labarai ta talabijin da hukumomin Dakar suka zarga da ingiza al'umma.