1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na karancin kwararrun ma'aikata

June 5, 2023

Ministocin harkokin waje da kwadago da ke ziyara a Brazil na fatan za su iya shawo kan karin kwararrun ma'aikata daga kasar don samun kyakkyawar makoma a Jamus.

https://p.dw.com/p/4SDrl
Berlin | Annalena Baerbock und Hubertus Heil reisen nach Brasilien
Hoto: picture alliance/dpa

A wannan Litinin din ce dai ministocin na Jamus guda biyu Annalena Baerbock da Hubertus Heil  suka fara wani rangadin aikin kwanaki uku, na zakulo ma'aikatan aikin jinya da kasar ke karanci a wannan kasa ta kudancin Amurka.

Baerbock ta ce tuni Jamus ta fara karbar ma'aikatan jinya da na bangaren aikin lantarki daga Brazil da Columbiya da hannu biyu, kuma suna muradin fadada wannan dangantakar.

A cewar Heil a daya hannun, a halin yanzu 'yan Brazil 200 ne ke aikin jinya a Jamus, sashin da ke fama da karancin kwararrun ma'aikata a cikin masana'antu da yawa.