1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta fara kwashe 'ya'yanta daga kasar Isra'ila

October 15, 2023

Jamus ta fara aikin kwashe 'ya'yanta da ke Isra'ila, daidai lokacin da wasu kasashe ke kokarin yin hakan saboda barkewar yaki tsakanin Isra'ilar da kungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/4XYEY

 

Rundunar sojin Jamus din ta Bundeswehr ta ce tuni wani jirgin yaki kirar A400M ya tashi da 'yan kasar su 51 daga filin jirgi na Ben Gurion da tsakar daren da ya gabata.

Akwai ma wani jirgin da ake sa ran ya taso da wasu mutum 29 'yan Jamus a wannan safiya ta Lahadi.

Jiragen da suka kwaso 'yan kasar daga Isra'ila dai jirage ne da suka kai kayan agaji, kamar yadda wani jami'i a majalisar dokoki da ke sashen da kula da al'amuran tsaro Wolfgang Hellmich ya fada.

Wani jirgin ma na uku zai tashi da nan gaba a yau.

A farkon wannan makon ne kuma babban kamfanin zirga-zirgar jirage na Jamus wato Lufthansa ya soke dukkanin jigilarsa zuwa Isra'ila.