1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus ta gayyaci jakadan Iran da ke kasar

April 15, 2024

Jamus ta gayyaci jakadan Iran a matsayin martani ga gayyatar jakadanta da na Burtaniya da kuma na Faransa da Teheran ta yi washegarin harin ramuwar gayya da ta kai wa Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4enBf
 Amir Saeed Iravani
Hoto: Yuki Iwamura/AFP/Getty Images

A yayin wani taron menema labarai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya ce jami'in diflomasiyyan Amir Saeid Iravani ya amsa wannan kira a safiyar Litinin sannan kuma ana ci gaba da sauraronsa. 

Karin bayani: Kasashen duniya sun caccaki Iran bayan harin Isra'ila

A daya gefe kuma shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke ziyara a China ya bukaci Isra'ila da ta bada hadin kai wajen dakile yaduwar yakin yankin Gabas ta Tsakiya, bayan da Iran ta cimma kudirinta na kai mata harin ramuwar gayya a karshen makon jiya.  

A yayin wani taron manema labarai, Mista Scholz ya kuma yaba da tallafin da hadakar kasashe kawayen Isra'ila suka bayar wajen dakile tasirin hare-haren, sai dai amma ya gargadi Isra'ilar da kadda ta kai abokan huldarta ga bango. 

Shugaban gwamnatin ta Jamus ya kuma kara da cewa a lokacin taron kasashe mafi karfin tattalin arziki na G7 ta kafar dibiyo, shugabanni sun yi kwakkwaran kashedi ga Iran da ta dakatar da barazanar da take yi wa Isra'ila.  

Karin bayani: An bude sabon babi a rikicin Iran da Isra'ila

To amma babban habsan sojojin Iran ya bi ta kafar kasar Swizland da ke wakiltar Amurka a kasar domin isar da sako ga Washigton kan cewa idan har ta yi kuskuren dafawa Isra'ila wajen kai mata wani sabon hari, Teheran za ta sauke fushinta a kan sojojin Amurkar da ke jibge a yankin Gabas ta Tsakiya.