1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta zargi Rasha ta satar bayanan rundunar sojojinta

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
March 4, 2024

Sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin Jamus da Rasha bayan da wasu bayanan sirri na rundunar sojoji suka fita ba tare da niyya ba. Amma Hukumar Leken Asirin Jamus ta fara gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

https://p.dw.com/p/4d9PI
Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da ministan tsaron Boris Pistorius sun saba kai wa sojoji ziyara
Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da ministan tsaron Boris Pistorius sun saba kai wa sojoji ziyaraHoto: William Noah Glucroft/DW

 

A ranar Jumma'ar makon da ya gabata ne, kafafen yada labaran Rasha suka saki wata murya da aka nada yayin wata tattaunawa ta wayar tarho mai tsawon mintuna 38, inda aka jiyo jami'an tsaron Jamus na tattauna batun bai wa Ukraine makamai da ma yiwuwar Kyiv ta kai farmaki a kan yankin Crimea da ya balle daga cikinta ya koma karkashin ikon Rasha. Wannan ya sanya mahukuntan Moscow bukatar bayani cikin gaggawa.

Karin bayani: Jamus ta yaba da fara janye sojojin Rasha

Jamus ta kira sakin wannan bayanai na sirri a matsayin satar bayanai da take bincike a kai, yayin da ministan tsaron kasar Boris Pistorius ya bayyana shi da wani mataki na yakin kafar Intanet da Rasha ke son kaddamarwa a kan Berlin. Pistorius ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani a karon farko kan batun, inda ya ce Moscow na son kawo rarrabuwar kawuna a Jamus.

 Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius na jajircewa wajen kare muradun sojojin kasarsa
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius na jajircewa wajen kare muradun sojojin kasarsaHoto: Britta Pedersen/dpa/picture alliance

Pistorius ya kara da cewa: "A bayyane yake cewa ya fi karfin nada tare da satar bayanan sojojin sama da kuma yada su, wani bangare ne na yakin kafar sadarwa da Putin ke son kaddamarwa babu shakku kan hakan. Hari ne na kafafen sadarwa da nufin yada bayanan bogi, batu ne na kawo rarrabuwa da kuma raina hadin kanmu. Kuma ya kamata mu mayar da martani cikin taka tsan-tsan, amma kuma tare da jajircewa."

Karin bayani: Kara karfi ga rundunar sojojin Jamus

Ita ma dai Rasha ta mayar da martani kan batun, inda mai magana da yawun Shugaba Rasha Dmitry Peskov ke cewa: "Bayan da aka nada na nuni da yadda ake tattauna batun shirin kaddamar da yaki a kan wani yanki na Rasha a tsakanin rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr, wannan ba ya bukatar wata fassara ta shari'a komai a bayyane yake karara. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewa, za su gudanar da bincike kan wannan batu. Muna fatan koma yaya ne koda ta kafafen yada laabarai ne, za mu samu bayanan abin da suka gano a binciken su."

Karin bayani: Cafke dan leken asirin Rasha a Jamus

Jakadan Jamus a Moscow Alexander Lambsdorff a kofar ma'aikatar harkokin wajen Rasha
Jakadan Jamus a Moscow Alexander Lambsdorff a kofar ma'aikatar harkokin wajen RashaHoto: Sergei Bobylev/TASS/IMAGO

Rahotanni sun nunar da cewa mahukuntan Moscow sun gayyaci jakadan Jamus a Rasha Alexander Graf Lambsdorff domin amsa wasu tambayoyi. Sai dai tuni Jamus ta mjusanta batun. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Jamus Christian Wagner ya shaida wa manema labarai cewa, akwai batun shirin ganawar jakadanta yana mai cewa: "A zahiri jakadanmu na ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Rasha, kasancewar an jima da shirya ganawar. Zan iya amsa tambayarka a takaice kan ko an aike masa sammaci ne da cewa a'a, ba zan yi karin bayani kan batun a nan ba."

karin bayani: Jamus: Diflomasiyya ce mafita a yakin Ukraine

An jiyo sojojin Jamus na tattauna batun aikewa da Ukraine makami mai linzami samfurin Taurus a bayanansu da aka nada, batun da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sanya kafa ya hambarar da shi a bainar jama'a. Sai dai duk da haka, fitar bayanan sirrin ya sanya Scholz cikin halin tasku, inda yake fuskantar zarge-zarge daga gida da waje. 'Yan adawa daga jam'iyyar CDU a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag na neman a gudanar da bincike domin samun karin bayani, abin da 'ya'yan jam'iyya mai mulki ta SDP suka nuna goyon bayansu kan matakin.