1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu aikin kashe gobara sun mutu a Girka

Abdourahamane Hassane
July 25, 2023

Ma'aikatar tsaron kasar Girka ta sanar da cewar matuka jiragen kashe gobara guda biyu sun mutu, bayan da jirginsu ya rikito a kudancin tsibirin Euboea.

https://p.dw.com/p/4UNwD
Griechenland I Waldbrände in Dervenochoria bei Athen
Hoto: Spyros Bakalis/AFP

Hatsarin ya afku ne a lokacin da daruruwan ma'aikatan kashe gobara da jiragen sama akalla hudu ke ta faman kashe gobarar a yankin. Sama da mako guda kenan da  yankuna da dama na Girka ke ci da wutar dajin. Yazuwa yanzu wata kungiyar  mai zaman kanta(WWF) ta ce wutar dajin ta  lalata kadada dubu 35,000 na gandun daji da ciyayi a kasar ta Girka.