1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Google zai inganta Intanet a Afirka

Suleiman Babayo MAB
October 6, 2021

Katafaren kamfanin Google wanda ya shahara kan neman bayanai a kafar zamani ta Intanet ya bayyana shirin zuba jari kimanin dalar Amirka milyan dubu a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/41L1q
Google Doodle Amaka Igwe
Hoto: Google/Data Oruwari

Kamfanin Google wanda ya yi matukar shahara kan neman bayanai a kafar zamani ta Intanet ya bayyana shirin zuba jari kimanin dalar Amirka milyan dubu a nahiyar Afirka nan da shekaru biyar masu zuwa, domin inganta hanyoyin samun intanet a nahiyar. A ciki kamfani zai saka waya ta karkashin teku domin hada nahiyar da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani inda wayar zai ratsa zuwa kasashen Tuirai ta karkashin tekun.

Sundar Pichai babban jami'in kamfanin na Google ya bayyana haka, inda ya ce wayar ta karkashin kasa za ta ratsa kasashen Afirka ta Kudu, da Namibiya gami da Najeriya zuwa tsibirin St Helena wanda yake gefen kasar Afirka ta Kudu wanda kuma har yanzu yake karkashin mullkin mallaka na Birtaniya.

Sannan kamfanin na Google zai samar da bashi mai sauki biya na dalar Amirka milyan 10 ga masu kananan sana'oi na da masu kirkiro ayyauka a kasashen Ghana, da Kenya, da Najeriya gami da Afirka ta Kudu, domin rage radadin da aka fuskanta sakamakon annobar cutar coronavirus da duniya ta fuskanta.