1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kasar Girka ta ceto bakin haure 145

Mouhamadou Awal Balarabe
June 22, 2023

Dubban bakin haure musamman daga kasashen Syria da Afghanistan da Pakistan nsun saba shiga kasar Girka daga kan iyakokin ruwa da kasa da Turkiyya. Amma Girka ta ceto wasu suka makale a tsibiri Evros.

https://p.dw.com/p/4SxZw
Girka ta saba ceto bakin haure da ke tangal-tangal a tekuHoto: Hellenic Coast Guard/REUTERS

Ba a bayyana sunaye ko kasashen da bakin hauren suka fita ba, amma hukomomi Girka sun tabbatar cewa masu fataucin mutane ne suka yi watsi da su a wannan tsibiri a kokarin shigar da su ta barauniyar hanya. Wannan dai ba shi ne karon farko da masu fasa-kwauri ke tura bakin haure zuwa yankin Girka ba.

Fadar mulki ta Athens ta saba zargin Turkiyya da barin bakin haure tsallakawa zuwa Girka. A farkon watan Yunin ma, wani yunkuri da Girka ta yi a wannan yanki, ya bada damar ceto mutane 91. Dubban bakin haure musamman daga kasashen Syria da Afghanistan da Pakistan ne suka saba shiga kasar Girka a shekarun baya-bayan nan daga kan iyakokin ruwa da kasa da Turkiyya.