1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance tsaro a arewacin Najeriya

Uwais Abubakar Idris
January 25, 2024

Tamkar dai tankade ne da rairaya aka yi inda aka zabo kwararru a harkar tsaro daga yankin arewacin Najeriyar kan matsalar ta'adanci da ta addabi yankin fiye da shekaru 15 ana fama da ita

https://p.dw.com/p/4bgWF
Matsalar tsaro ta tagaiyara jama'a a jihar Borno
Matsalar tsaro ta tagaiyara jama'a a jihar BornoHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Daya daga cikin matsalolin da aka duba shi ne zargin rashin hadin kai da aiki tare a tsakanin jami'an tsaron Najeriyar, inda ake kasa daukar matakin dakile hari har sai ya afku. Janar Christopher Gwabin Musa shi ne babban hafsan tsaron Najeriya.

Mun san cewa ba hukumar da za ta iya yin wannan aiki ita kadai, dole a hada kai a yi aiki tare. Matsalar da aka samu ba'a dauki mataki da wuri ba, an bar matsalar sai da ta lallace, to amma Allah yana tare da damu.

Wasu 'yan gudun hijira a jihar Borno
Wasu 'yan gudun hijira a jihar BornoHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Karin Bayani: Matsalar tsaro ta yi kamari a sassan Najeriya

Mahalarta taron da suka hada da Janar Abdulsallami Abubakar tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja sun shafe kwanaki biyu suna tattaunawa don samo mafita.

Daukacin gwamnonin jihohin da suke fama da matsala tsaron sun hallarci taron, in banda kalilan da suka turo wakilai. Dr Dikko Radda

'Yan gudun hijira a Dikwa
'Yan gudun hijira a DikwaHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Karin Bayani:Najeriya: Fargaba saboda matsalar tsaro

Cusa siyasa koma dai maida batun rashin tsaron sana'a batutuwa biyu da aka dade ana bayyana faruwarsu a harkar rashin tsaron Najeriyar da ke bukatar rarrabe aya da tsakuwa. Farfesa Attahiru Jega na cikin kwararrun ‘yan boko daga yankin arewacin Najeriyar da suka yi tsokaci.

Tun da farko dai mataimakin shugaban Najeriya Kasim Shettima ya bayyana cewa kawo karshen matsalar tsaro shi ne muhimmin aikin da gwamnati ta sanya a gaba. Za'a mika dukkanin shawarwarin da aka cimma ga gwamnati domin daukar matakan da suka dace.