1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu na ci gaba da soke wasu zabuka a Najeriya

September 19, 2023

Akalla 'yan majalisar dattawa biyar ne alkalai suka ce su tafi gida baya ga 'yan majalisar wakilai 26 da wasu 'yan doka na jihohi da ba su kirguwa cikin shari'u na zabuka da ke gudana a cikin tarrayar Najeirya.

https://p.dw.com/p/4WYjH
Nigeria | Kommunalverwaltung Gesetz in Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Sama da karrarakin zabe 300 ne kotunan zabe na Najeriya ke sauraro, kuma ke shirin yanke hukunci kansu kafin karshen watan Satumba da ke zaman wa'adin kare shari'un zabuka a daukacin kasar.  Babu asara ko da guda daya har ya zuwa yanzu kama daga zaben shugaban kasa Bola Tinubu i zuwa na gwamnoni. Amma gidan 'yan dokar na zaman ba sabun ba cikin kasar, da ake zargin hada baki a tsakanin alkalan shari'un da masu takama da siyasa na kasar. Tun ba'a kai ko'ina ba, akalla kaso 10% na zabukan kasar ne aka soke da nufin sake su, ko kuma sauya wanda ya lashesu.

Karin bayani:Kotu za ta yanke hukunci kan zaben Najeriya na 2023

Kotu ta wanke Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga targin magudin zabe
Kotu ta wanke Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga targin magudin zabeHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Dr Umar Ardo da ke zaman dan takara na jam'iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Adamawa, ya ce sabon sauyin na da ruwa da tsaki a aiken tsoro a zuciyar alkalan zaben a matakai daban-daban.Daga dukkan alamu dai, idanun da ke gaban alkalan zai yi nisa cikin fagen siyasa ta kasar da ke nuna alamun ko namu ko kafar katako. 

Karin bayani:Najeriya: Kotun sauraren kararrakin zabe ta fara zama

Sabon sauyin na iya kaiwa ya zuwa ga kara ingancin zaben da kila sauya makoma ta daukacin Najeriya da ke neman ingantar tsarin dimokuradiyya. Barrister Buhari Yusuf da ke zaman lauyan mai zaman kansa a Abuja, ya ce sabuwar rawar alkalan na da ruwa da tsaki da sauyin dokokin zabe na kasar. A cikin wannan mako ne aka fara tabo zaben gwamnonin jihohin kasar 28 da ya gudana a Maris.