1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisun dokokin Najeriya sun koma bakin aiki

Uwais Abubakar Idris/ASSeptember 20, 2016

Rigingimun da suka kuno kai a majalisar wakilan Najeriya sun ci gaba da mammaye harkokin majalisar a daidai lokacin da suka koma aiki bayan kamala dogon hutu.

https://p.dw.com/p/1K5bE
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera


'Yan majalisar dai sun cika zauren nasu makil domin fara zamansu don tinkarar zarge-zargen da suka taso aringizo da cushe a kasasfin kudin na 2016 wanda takwaransu Abdulmumini Jibril ke cigaba da yayatawa. To sai di bayan fara zaman kakakin majalisar Yakubu Dogara ya dage zaman majalisar saboda mutuwar daya daga cikinsu amma a share guda rikicin na da sake tirnikewa inda Abdulmumini Jibril ya ce akwai sabbin abubuwan da ya bankado inda ya ce dole ne a dau mataki koda kuwa za'a dakatar da shi daga majalisar.

A share guda kuma batun cire Alhassan Ado Doguwa daga matsayinsa na shugaban 'yan majalisa daga arewa maaso yammacin Najeriya ne ya rika yawo tsakanin 'yan majalisar idan masu goyon bayan shugaban majalisar musamman na yanki arewa maso gabashi kasar suka ce wannan zance ba haka ya ke ba domin a cewar su ko kusa ba a wani shiri da majalisar ke yi na raba Alhassan Doguwa din da matsayinsa na jagoran 'yan majalisa daga yankin arewa maso yamma. A bayyane ta ke a fili cewa rikici a kan zargin aringizo a majalisar wakilai za ta sanya kwasar ‘yan kallo a tsakanin Abdulmumini Jibrin da sauran ‘yan majalisar da ke murza gashin baki na sai sun yi maganin wannan batu da suke wa kallon zargi ne da ba za su lamaunta ba.
Can a majalisar datawa kuwa shugabanta an maida hankali ne a kan koma bayan tattalin arziki da ke fuskantar tarayyar Najeyar inda shugaban majalisar Bukola Saraki ya ce a kansa ne za su maida hankali kacokan a zaman majalisar domin tsara shawarwari da nufin samar da gyara.

Nigeria Bukola Saraki
Bukola Saraki ya ce majalisar dattawa na son a warware kalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fama da shiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba
Nigeria Symbolbild Korruption
Zargi kan cushe da aka yi wa kasafin kudin 2016 a daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin 'yan NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba