1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ASUU ta tsawaita yajin aiki a Najeriya

May 9, 2022

A wani abun da zai iya ta'azzara rikici a tsakanin malaman jami'oin Najeriya da gwamnati, kungiyar malaman ta tsawaita wa'adin yajin aikinta zuwa wasu makonni 12.

https://p.dw.com/p/4B2Jc
Nigeria Studenten in Jos
Hoto: picture-alliance/epa/Ruth McDowall

A wannan Litinin din ce ASUU da ta gudanarwa da wani taron majalisar zartarwarta a birnin Abuja dai ta ce, bayan nazarin yajin aiki na gargadi na tsawon watanni guda biyu da ya kare, bata da zabi face tsunduma cikin wani sabon yajin aikin na makonni 12.

Dr Abdulkadir Mohammed da ke zaman dan majalisar koli na kungiyar daya kuma a cikin mahalarta taron ya ce, babu alamun gaskiya a bangaren gwamnatin tarayyar Najeriyar na warware matsalar malaman jami'oi.