1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga sabuwar jamhuriya a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou Usman Shehu Usman
July 22, 2023

Majalisar koli ta mulkin soji a Mali ta amince da sabon kundin tsarin mulki duk da korafe-korafen da masu adawa da zabensa suka shigar a gaban kotu da zargin tafka magudi.

https://p.dw.com/p/4UGuF
Mali | Übergangspräsident Assimi Goïta
Shugaban majalisar mulkin soji ta wucin gadi a Mali Kanar Assimi GoïtaHoto: Präsidentschaft der Republik Mali

Shugaban gwamnatin mulkin soji ta rikon kwarya a Mali Kanar Assimi Goïta, ya rabbata hannu kan sabon kudin tsarin mulki, da 'yan kasar suka zaba a makwannin da suka gabata duk da korafe-korafen da masu adawa da zaben suka shigar a gaban kotu, suna kalubalantar zaben da suka ce an yi sa ne a wani bangare na kasar kawai.

Kotun tsarin mulkin kasar ta halasta kaso 38 da digo 23 cikin 100, na adadin 'yan kasar da suka fito kada kuri'ar, duk da yake tana cewa adadin ya yi kasa idan aka yi la'akari da yadda ake tafiyar zabe a kasar, da ma soke wasu runfunan zaben da ta ce ta yi kafin sakamakon.

Rattaba hannu kan kudurin amincewa da sabon kudin tsarin mulkin na Mali da fadar mulki ta birnin Bamako ta yi, guda ne daga cikin alkawuran da sojojin da ke kan madafan iko shekaru ukun da suka gabata suka yi na sake mika mulki a hannun wata gwamnatin farar hula nan da shekarar 2024.